Join Our Channels
Get important updates, news and useful information directly.

JAMB Hausa Syllabus PDF Download

Share:
X W T
JAMB Hausa Syllabus PDF

HAUSA

GENERAL OBJECTIVES

The aim of the Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME) syllabus in Hausa is to prepare the candidates for the Board’s examination. It is designed to test their achievement of the course objectives, which are to enable the candidates to:

  1. Acquire the ability to read and write competently in the Hausa language;
  2. Know the basic features of Hausa language (syntax, phonology, morphology and semantics).
  3. Have the basic knowledge of oral and written Hausa literature;
  4. Have the ability to appreciate the culture, customs and institutions of the Hausa people;
  5. Have the ability to translate competently from English to Hausa.

The syllabus covers the following areas:

  1. Harshe (Language)
  2. Al’adu (culture)
  3. Adabi (Literature); oral and written literature.

CIKAKKEN BAYANIN MANHAJA (DETAILED SYLLABUS)

1. Harshe (Language)

(a) Ƙa’idojin Rubutu (Orthography);

alphabetization, spelling, rules of word merger and division, punctuation and paragraphing all in line with standard Hausa.

Candidates should be able;

  1. recognize the basic Hausa orthographical rules;
  2. apply the Hausa orthographical rules;
  3. identify linguistic errors, such as; grammar, wrong choice of words, wrong spelling etc.

(b) Auna Fahimta (Comprehension);

contextual questions from short unseen passages of about 200 words.

Candidates should be able;

  1. read written Hausa texts;
  2. comprehend Hausa text in a given context;
  3. interpret various meanings and functions of words in a given text;
  4. acquire sufficient vocabulary;
  5. recognize central issues in a given text;
  6. draw conclusions based on available evidence in a given text.

(c) Tsarin Rubutun Insha’i (Composition Techniques);

argumentative, descriptive, dialogue, expository, narrative and letter writing.

Candidates should be able;

  1. acquire the knowledge and techniques of composition writing in Hausa;
  2. recognize the different segments of composition in Hausa;
  3. recognize the different types of Hausa composition.

(d) Fassara (Translation)

  1. Ire-iren fassara (types of translation)
  2. Ƙa’idojin fassara (rules of translation)
  3. Matsalolin fassara (problems of translation)
  4. Dabarun fassara (techniques of translation).

Candidates should be able;

  1. translate proverbial and idiomatic expressions and new words from English to Hausa;
  2. recognize the different types of translation;
  3. understand the basic techniques of translating proverbial and idiomatic expressions and new words into Hausa;
  4. identify the problems of translation into Hausa.

(e) Tsarin Sauti (Phonology)

  1. consonants – production and classification in terms of phonation, place and manner of articulation;
  2. vowels – production and classification in terms of position of tongue and lips; monophthongs and dipthongs;
  3. tone – e.g. high, low and falling tones;
  4. syllable structure – syllable types, e.g. open and close syllables, light and heavy, syllables; syllabic categories of words – monosyllabic, disyllabic, etc.
  5. vowel length – long and short vowels;
  6. phonological processes – e.g. assimilatory: palatalization, labialization and vowel harmony; non-assimilatory: insertion and deletion.

Candidates should be able;

  1. analyse the process of sound production and combination of sounds to form meaningful words in Hausa;
  2. appraise the importance of vowels in determining meaning;
  3. distinguish between the phonetic attributes of sounds;
  4. recognize the number of syllables and their types in a word;
  5. analyse the phonological processes in Hausa.

(f) Ƙirar Kalma (Morphology)

  1. roots and stems;
  2. affixation – e.g. prefix, infix suffix and their derivational and inflectional functions;
  3. gender and number inflections;
  4. derivation of nouns and adjectives from verbs; adjectives and verbs from nouns.

Candidates should be able;

  1. explain the roots and stems of Hausa words;
  2. explain the inflectional process in Hausa word formation;
  3. explain the derivational process of word formation in Hausa;
  4. differentiate between the two morphological processes.

(g) Ginin Jumla (Syntax):

  1. word classes-e.g. nouns, pronouns, verbs, adverbs, adjectives, prepositions, conjunctions, interjections and ideophones;
  2. grammatical categories – e.g. tense and aspect (general and relative past: general and relative continuous, first and second future, habitual); mood (subjunctive and negative); gender (masculine, feminine and neuter) and number (singular and plural);
  3. sentence structure – e.g. verbal sentence, nominal phrase + verbal phrase and their components, non-verbal sentence: nominal phrase + stabilizer, nominal phrase+ compliment + stabilizer, nominal phrases + continuous frame (yana../yake…) (+da) + nominal phrase;
  4. sentence types – e.g. simple sentences, compound sentences and complex sentences;
  5. clauses – types (e.g. relative and subjunctive); functions (e.g. main and subordinate).

Candidates should be able;

  1. analyses the processes governing word combination to form phrases; clauses and sentences in Hausa
  2. detect linguistic errors in the grammar;
  3. recognize ideas or thoughts in written form;
  4. construct grammatical sentences for effective communication;
  5. use the appropriate tenses in spoken and written Hausa;
  6. use the appropriate gender and number in spoken and written Hausa;
  7. differentiate between types of sentence structure;
  8. distinguish between nominal and verbal phrase;
  9. distinguish between types of sentences;
  10. compare types of clauses.

(h) Ma’ana (Semantics)

  1. lexical aspects of word meaning – e.g. ambiguity, synonym and antonym;
  2. figures of speech – aspects of specialized meanings of words and phrases, e.g. idioms, proverbs etc.

Candidates should be able;

  1. analyses the mechanisms of generating meanings in Hausa;
  2. build up their vocabulary;
  3. recognize the various meanings and functions of sentences in communication;
  4. use words and sentences suitable for a particular purpose;
  5. construct meaningful sentences for effective communication.

(2) Al’adu (Culture)

(a) Rayuwar Hausawa (Hausa customs);

  1. haihuwa (birth) –ɗaukar ciki da goyon ciki da haihuwa da shayarwa da al’adun makon farko na haihuwa da wanka da ɓanti da yaye da kaciya da samartaka;
  2. aure (marriage) – ire-irensa da nema da baiko da ɗaurin aure da biki da zaman aure da saki da zawarci;
  3. mutuwa (death) – faɗar mutuwa da wanka da salla da jana’iza da zaman makoki da sadaka da takaba da gado;
  4. tasirin zamani akan rayuwar Hausawa.

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarabawa su iya:

  1. bayyana al’adun da ke tattare da ɗaukar ciki har zuwa samartaka;
  2. bayyana tasirin zamani a kan haihuwa;
  3. bayyana al’adun neman aure har zuwa zawarci;
  4. bayyana tasirin zamani akan aure;
  5. bayyana hanyoyin faɗar mutuwa zuwa rabon gado;
  6. bayyana tasirin zamani akan mutuwa;
  7. tantance ma’ana da ire-iren tasirin zamani.

(b) Zamantakewa (Social Institutions)

  1. tsarin zaman iyali da zaman gandu da dangantakar kishiyoyi da ‘yan uwantaka da barantaka da agolanci;
  2. maƙwabtaka;
  3. aikin gandu da na gayya;
  4. abota da ƙawance;
  5. gaisuwa da karamci;
  6. tasirin zamani a kan zamantakewa.

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. bayyana tsarin dangantaka da mu’amala tsakanin iyali;
  2. bayyana muhimmancin zamantakewa a tsakanin Hausawa;
  3. tantance ire-iren tasirin zamani a kan al’adun zamantakewa.

(c) Sana’o’in Gargajiya (Traditional Occupations)

  1. ire-irensu – noma da ƙira da jima da kasuwanci da wanzanci da sassaƙa da farauta da dukanci da saƙa da kitso da rini da fawa da fafar ƙorai, da sauransu;
  2. yanayinsu – hanyoyin gadon su da kayayyakin yin su da matakan tafiyar da su da muhimmancinsu;
  3. kayayyaki ko amfanin da suke samarwa;
  4. sarautunsu;
  5. sana’o’i masu dangantaka da jinsi – aikatau da ƙwadago; kitso da aski.;
  6. tasirin zamani a kan sana’o’in gargajiya.

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. tantance ɗabi’un masu sana’a;
  2. tantance kayayyakin da ake sana’antawa;
  3. tantance sana’o’in maza da na mata;
  4. zayyana kayayyakin sana’o’in;
  5. tantance hanyoyin gadon sana’o’in;
  6. zayyana amfanin kayayyakin sana’o’in;
  7. bayyana sarautun sana’o’in;
  8. bayyana muhimmancin sana’o’in;
  9. tantance tasirin zamani akan sana’o’in.

(d) Kayayyakin Buƙatun Rayuwa (Material Culture)

  1. na buƙatun cikin gida (household) – tufafi da karikitan cikin gida;
  2. na sauran buƙatu (others) – gine-gine da girke-girke da sauransu;
  3. tasirin zamani a kan kayayyakin buƙatu.

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. tantance kayayyakin buƙatun rayuwa na hausawa;
  2. tantance amfanin kayayyakin buƙatun rayuwa na Hausawa;
  3. tantance tasirin zamani a kan kayayyakin buƙatun rayuwa na Hausawa.

(e) Bukukuwa da Wasanni (Hausa Festivities and Recreational Activities):

  1. na addini (religious) – irin su bikin salla da takutaha (sallar gani) da cika-ciki da saukar karatu;
  2. na gargajiya (traditional) – irin su kalankuwa da buɗar dawa, da bikin shan kabewa;
  3. na sana’a (occupational) – bikin kamun kifi da dambe da kokawa da wasan farauta da wasan maƙera da hawan ƙaho;
  4. na nishaɗi – sukuwa;
  5. na yara (children’s games) –irin su shalle da kulli-kurciya da a-sha-ruwan-tsuntsaye da gaɗa da carafke;
  6. tasirin zamani kan bukukuwa da wasanni.

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. zayyana ire-iren wasanni da bukukuwan Hausawa;
  2. nuna mahimancinsu;
  3. nuna yadda za a adana su kada su ɓace;
  4. nuna yadda ake gudanar da su;
  5. nuna tasirin zamani a kan bukukuwa da wasanni.

(f) Camfe-camfe da Bauta (Traditional Beliefs and Worship):

  1. camfe-camfe irin su kangida da camfi, da kambun baka da maita;
  2. bauta irin su bori da da tsafi;
  3. tasirin zamani a kan camfe-camfe da bauta.

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. tantance ire-ire da hanyoyin aiwatar da su;
  2. bayyana amfaninsu;
  3. bayyana rashin amfaninsu.
  4. bayyana tasirin zamani a kansu.

(g) Sarautun Gargajiya (Traditional Authority)

  1. ire-iren su – sarakuna da hakimai da dagatai da masu unguwanni;
  2. na bayin sarki – shantali da jakadiya da baraya da sauransu;
  3. masu alaƙa da addini; irin su liman da alƙali;
  4. ayyukansu.
  5. tasirin zamani a kan sarautun gargajiya.

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. zayyana su ta fuskar ire-iren muƙamai;
  2. zayyana matakan muƙamai;
  3. tantance aikin kowane mai muƙami;
  4. tantance mahimmancin kowane muƙami.
  5. bayyana tasirin zamani a kansu.

(h) Magungunan Gargajiya (Traditional Medicine)

ire-iren su;

  1. na gargajiya: sassaƙe-sassaƙe da sawyoyi da na gari da na ruwa;
  2. na addini: layu da rubutu da ɗibbu da duba;
  3. hanyar amfani da su – sha da shafawa da surace da turare da shaƙawa da taunawa da tsotsawa da ɗaurawa da liƙawa da ratayawa;
  4. tsarin amfani da su awo da kimantawa;
  5. ayyukansu – riga-kafi da warkarwa;
  6. tasirin zamani a kansu.

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. karkasa ire-iren magunguna;
  2. zayyana hanyoyin amfani da su;
  3. fito da amfaninsu;
  4. nuna tasirin zamani a kan su.

(3) Adabi (Literature)

I. Adabin Baka (Oral Literature)

(a) Zuben Baka (Narratives):

Irin su tatsuniya da almara da hikaya da ƙissa da tarihi da sauransu.

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. tantance nau ‘o’in zuben baka;
  2. amfani da kalmomin da suka dace da kan labari.

(b) Maganganun Azanci (Folk – sayings);

Irin su take da kirari da habaici da zambo da karin magana da kacici-kacici da salon magana da adon magana da sauransu.

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. tantance sigogi da bayyana hanyoyin amfani da su;
  2. naƙalta da amfani da kalmomin da suka dace da maganganun azanci.

(c) Waƙoƙi na baka (Oral songs):

  1. ire-iren su – na fada da na jama’a da na maza da na sha’awa da sauransu:
  2. turke (jigo) da salo da zubi da tsari da mawaƙi da kayan kiɗa da abin da aka waƙe.
  3. waƙoƙin aiki: na niƙa da daɓe da na daka da na talla da sauransu;
  4. Waƙoƙin yara (maza da mata); na aure da na dandali da sauransu;

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. tantance ire-iren waƙoƙin baka;
  2. tantance masu yin ire-iren waƙoƙin;
  3. rarrabe siga da turke (jigo) da salo da zubi da kayayyakin aiwatar da su.
  4. tantance nau’o’in waƙoƙin aiki;
  5. tantance masu yin waƙoƙin aiki;
  6. bambance sigogin waƙoƙin yara.

(d) Wasannin Kwaikwayo Na Gargajiya (Traditional Drama):

i. Na yara:

  1. ire-irensu - langa da wasan ’yartsana da tashe da wasan gauta da dokin kara da sauransu;
  2. yadda ake yin su.
  3. muhimmancinsu

ii. Na manya:

  1. ire-irensu - ‘yan kama da kalankuwa da hoto da wowwo da tashe, da sauransu;
  2. yadda ake yinsu;
  3. muhimmancinsu

Lallai ne waɗanda za su rubuta jarrabawa su iya:

  1. tantance sigogin wasannin kwaikwayo na gargajiya.
  2. tantance hanyoyin gudanar da wasannin kwaikwayo na gargajiya;
  3. fito da muhimmancin wasannin kwaikwayo na gargajiya;
  4. fayyece bambancin wasan kwaikwayo na yara da na manya.

II. Rubutaccen Adabi (Written Literature)

Zube (Prose)

i. Turmin Danya

Lallai ne masu ɗaukar jarabawa su iya:

  1. tantance siga da tsari da jigo da salo da taurarin cikin littafin zube tare da nazarin su;
  2. naƙaltar ƙa’idojin rubutu yayin karanta rubutun zube;
  3. naƙaltar ma’anonin kalmomi da na jumloli domin fahimtar labari;
  4. tantance muhimman saƙonni a cikin labari da yanke hukunci game da labarin.

Waƙa (Poetry)

i. Waƙoƙin Hausa

Lallai ne masu ɗaukar jarabawa su iya:

  1. fahimtar jigo da salo da siga da zubi wajen nazarin zaɓaɓɓiyar waƙa;
  2. yin la’akari da ƙa’idojin rubutu musamman na waƙa;
  3. tantance ma’anonin kalmomi da na jumloli wajen nazarin waƙa;
  4. danganta amfani da kalmomi da jumloli da saƙon waƙa;
  5. tantance muhimman saƙonni a cikin waƙa da yanke hukunci game da ita.

Wasan Kwaikwayo (Drama)

i. Abin Da Kamar Wuya...

Lallai ne masu ɗaukar jarabawa su iya:

  1. tantance yanayin wurin wasa da jigo da salo da ‘yan wasa da siga da tsarin rubutaccen wasan kwaikwayo da aka zaɓa don nazari;
  2. la’akari da muhimmancin ƙa’idojin rubutu wajen fitar da ma’ana;
  3. naƙaltar ma’anar kalmomi domin fahimtar wasa;
  4. tantance muhimman saƙonni a cikin wasa da yanke hukunci game da saƙonnin.

HAUSA

LIST OF SET TEXTS FOR THE UTME 2022 – 2025

A. WRITTEN LITERATURE:

ZAƁAƁƁUN LITTATTAFAI (PRESCRIBED TEXTS)

GENRE TITLE AUTHOR PUBLISHER
PROSETurmin DanyaKatsina, S. I.NNPC, Zaria, 2011
DRAMAAbin Da Kamar WuyaBugaje, H. M.ABU Press Ltd, Zaria, 2018
POETRYWaƙoƙin HausaWali, N.S. da wasuNNPC, Zaria, 1982

B. ORAL LITERATURE

GENRE TITLE AUTHOR PUBLISHER
PROSEMu Sha DariyaTofa, B. O.NNPC, Zaria, 2018
DRAMAWasannin TasheUmar, M. B.NNPC, Zaria, 2009
POETRYJagoran Nazarin Waƙar BakaGusau, S. M.Benchmark Publishers Ltd, 2003

C. LANGUAGE

TITLE AUTHOR PUBLISHER
Sound System And GrammarSani, M. A. Z.U.P.Plc, Ibadan, 2000

D. CULTURE

S/N TITLE AUTHOR PUBLISHER
1.Rayuwar HausaCSNL/BUKNelson, Lagos, 1980
2.Hausa CustomsMadauci, I.NNPC, 1985

E. GENERAL REFERENCE BOOKS

S/N TITLE AUTHOR PUBLISHER
1.Exams Focus Hausa LanguageSani, M.A.ZU.P.PLC, Ibadan, 2000
2.Darussan Hausa 1 – 3Yahaya, I. Y. et alU.P.PLC, Ibadan, 1992
3.Rayayyen Nahawun HausaJunju, M.H.NNPC,Zaria, 2010
4.An Introduction to Hausa GrammarM.K.M. GaladanciLongman Nigeria, 1984
5.Jagoran Nazarin Kagaggun LabaraiMukhtar, I.A.J. Publishers, Kano, 2002
6.Rabe-Raben Adabi Da Muhimmancinsa Ga Rayuwar HausawaDangambo, A.Triump Publishing Company, Kano, 1984
7.Harshe Da Adabin Hausa A KammaleIsmaila, J and Tanimu. M.YSpectrum Books, Ibadan, 2007
8.Labaru Na Da Da Na Yanzu
NNPC, 1985
9.Zaman Mutum Da Sana’arsaE.M. Rimmer, et al.NNPC, Zaria, Reprinted 2002
10.Zaman HausawaAlhassan, H. et alIslamic Publication Bureau, Lagos, Reprinted 1988
11.Waƙa A. Bakin Mai ItaCSNL, BUK, KanoNNPC, Zaria, 2006

RECOMMENDED TEXTS

Almajir, T.S. et al. (2016) Idioms in English – Hausa, Zaria; ABU, Press

Galadanci, M.K.M. (1976), Introduction to Hausa Grammar, Zaria: Longman

Junju, M.H. (1980), Rayayyen Nahawun Hausa, Zaria: NNPC

Muhammad, Y.M. (2005), Fassarar Hausa, Zaria: ABU Press

Sani, M.A.Z. (1999), Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa, Ibadan: UP Plc

Sani, M.A.Z. et al (2000), Exam Focus: Hausa Language, Ibadan: UP Plc

Skinner, N. (1977), Grammar of Hausa, Zaria: NNPC

Yahaya, I.Y. et al (1992), Darussan Hausa Don manyan makarantun sakandare 1 – 3, Ibadan: UP Plc

B. ADABI DA AL’ADU (LITERATURE AND CULTURE)

Bichi, A.Y. (1979), Waƙoƙin Bikin Aure, Lagos: Nelson

Dangambo, A. (1984), Rabe – Raben Adabin Baka da Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa, Kano: Triumph Publishing Company

Gusau, S.M. (1991), Makaɗa Da Mawaƙan Hausa, Kaduna: Fisbas Media Service

Ibrahim, M.S. (1977), Kowa Ya Sha Kiɗa, Zaria: Longman

Madauci, I. et al (1992), Hausa Customs, Zaria: ABU Press

Umar, M.B. (1976), Ɗanmaraya Jos Da Waƙoƙinsa, Ibadan: OUP

Umar, M.B. (1977), Wasannin Tashe, Zaria: NNPC

C. ƘAMUSAI (DICTIONARIES)

Bargery G.P. (1951), A Hausa – English Dictionary and English-Hausa Vocabulary London: OUP

Newman, R.M. (1997), An English-Hausa Dictionary, Ibadan: Longman

Newman and Newman (1977), Sabon Ƙamus Na Hausa Zuwa Turanci, Ibadan: UPL

Skinner, N. (1993), Kamus Na Turanci Da Hausa, Zaria: NNPC

CSNL: (2006), Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero Zaria: ABU Press


PDF
Hausa.pdf
PDF Document
↓ Download File
UTME2027 Editorial Team

UTME2027 Editorial Team

Editorial Team

The UTME2027 Editorial Team publishes accurate, timely and well-researched JAMB news, admission updates, CBT preparation guides and official educational information for Nigerian students. Every article is reviewed before publication to ensure accuracy and clarity.

View all articles →

← Previous Article JAMB Government Syllabus 2027 PDF Download
Next Article → JAMB History Syllabus 2027 PDF Download

Related Articles